jerin bayanai

Thursday, 12 October 2017

WASU DAGA SIFFOFIN SO NA GASKIYA.

WASU DAGA SIFFOFIN SO NA GASKIYA.

akwai alamomin so nagaskiya dayawa dan haka ataqaice zan kawo su.

Shi so nagaskiya yasamo asali ne daga son Allah da manzon sa wato saurayi ko budurwa ana so su so junan su dan Allah

kaso ko ki so masoyinki dan kyawawan halayen sa da dabi'un sa.
Ko dan jajurcewar abun so wajen addini.

Sannan so dan Allah bai fiya faruwa ko qulluwa a lokaci daya ba ,yawanci yakan dau lokaci ana nazari da karantar abun da za aso din har a gamsu da halayen sa da dabi'unsa masu kyaune sannan haka yake ginuwa a zuciya a tsanake kafin a furtashi wato yabayyana afili.

Akan yishi batare daa la akari daa wata dangantakaba ko sonkai kuma baa ruwan ido acikin sa akaan tsai da saaurayi daya ko budurwaa daya sannan ba canji.

Yana da wuya a rabu kuma Koda anrabu akan dau tsaahon lokaci kafin amaye gurbin sa da wani har mutum yakan yanke qaunar samun wani masoyin kamar nada din.

Yana daga siffar so nagaskiya shine SAURIN WARWARE MATSALA INTAFARU A TSAKANIN MASOYA
domin cike yake da tausayin juna da hakuri da juriya DOMIN MASOYA ARANSU SUN YADDA BA SOYAYYA KADAI SUKEYI BA A A IBADA SUKEYI.
KUMA DAN ALLAH shi yasa da matsala tasamu sai ai saurin warware ta batare da bata lokaciba harma mutane suna zatn ba kwafada a juna.

Akan yimamkin shakuwar masoyan da suke soyayya tagaskiya domin abayyana yake sunayi ne badan kudiba badaan matsayiba bakuma dan SHA'AWAR JUMA'IBA KO KYAU TARE DACEWA SUNA JIN SHA'AWAR AMMAA HAKA ZASU DAURE SU JUREWA JUNA HAR SUYI AURE.

MASOYA NAGASKIYA SUNA MATUQAR KISHIN JUNAN SU,SOYAYYAR SU BATARUFE MUSU IDO IDAN DAYAN SU YAIBADAIDAAIBA TO DAYAN YAKANYIMASA NASIHA SHIKUMA YAKAN KARBI NASIHAR.

kasancewar anginashi akan tsoran Allah da fahimtar juna hakan yasa yake da karko kuma zaiwuya a raba irin wadannan masoya domin ruhinsu yazama daya sunzama tamkar jiki daya.

Akoda yaushe sukan yiwa juna kyakkyawan zato abayn ido ko agaban ido dan haka munafurcin muna fuki baai tasiri.

Yan uwa irinwannan so idan akayi aure dashi tofa shine aljannar duniya DOMIN MASOYA SUNA TSUFANE AMMA SOYAYYAR NA QARUWA.
domin damacan anginashine akan tubali mekyau wato anason juna dan Allah kuma anfahimci juna ITAKUWA SOYAYYAR ALLAH BATA QAREWA BATAA RAGUA SAIDAI TA QARU. mutu karaba kenan.

Irinwannan soyayyar akarasa ayau shi yasa aure baya albarka baya qarko domin dayawan masoya a yau sunayin soyayya ne ba dan Allah ba dukdaccewa abaka kowa zai yi da awar dan Allah yake son abun kaunarsa amma ahakikanin gaskiya yana soyayyane imma dan
kyan fuska, ko kwadayin kudin iyayenta wato zai sha gara kodan matsananciyar sha'awar juma'i.
Shiyasa da anyi aure sai kaga lokaci kadan aure ya mutu.

*ABUBUWA BIYU MASU HIMMANCI DAYA KAMATA MUYI LA AKARI DASU A SOYAYYA.

1 SO DAN ALLAH
2 FAHIMTAR JUNA

ALHAMDULILLAH.
09073717289

No comments:

Post a Comment

https://shaykhulislaam.files.wordpress.com/2010/12/criterion.pdf

https://shaykhulislaam.files.wordpress.com/2010/12/criterion.pdf