jerin bayanai

Thursday, 5 October 2017

BAMBANCIN AUREN DA DANA YANZU. 09073717289

BAMBANCIN AUREN DA DANA YANZU.

Haqiqa ansami gagarimin banbanci tsakanin aure a zamanin da dana yanzu ,in Allah yaso zamu danyi bayani akan hakan.

*1 Azamanin da ALLAH SWT ya Albarkaci aure sosai fiye da yau, DALILIKUWA aure bashida wahala sosai kamar a yau ,MANZON ALLAH S.A.W YACE MAFIFICIYAR MACE WACCE ZATA SHIGA ALJANNAH ITACE WACCE TA TSARE KANTA DAGA AIKIN ALFASHA KUMA BA ASHA WAHALAR NEMAN AURENTABA.manzan Allah s.a.w yayi gaskiya Azamanin da aure bashi da wahala kama a yau ,da TARE DA HAKAN SAIKAGA MACE ANYI AUREN TAZAUNA KUSAN SHEKARU 20 ,KO 30 amma mace bata taba yaji ba koda sau 1,tare dacewa ba asha wahalar neman aurentaba SAKAMAKO ALLAH SWT YA ALBARKACI AUREN,. Amma abun takaici a yau zaka ga aure ansha wahalarsa fiye daqima saurayi yasha wahala dakyar yasamu yayi auren yakashewa budurwa dukiya metarin yawa AMMA ABUN HAUSHI SAIKAGA DA ANYI AURE SHEKARA 2,3 SAIKAJI ANFARA YAJI WANI MA KO SHEKARA AUREN BAYAYI ZAKAJI YAMUTU. sakamakon Allah swt ya zare albarkarsa saboda ansha wahala wajen neman aure.

In munfahimci HADISINNAN NA ANNABIN RAHA S.A.W ,ASHE KENAN KUSKURNE DA MUMMUMAR FAHIMTA,DA HUDUBAR SHEDAN YAKEWA MASU CEWA WAI INSAMARI BA SUSHA WAHALA WAJEN NEMAN AUREBA BASA IYA RIQE MACE . wannan kuwa qaryane domin ayau da akafi wahala a aure a yaune akafi mutuwar aure da yaji. Sakamakon da da ba ashan wahalar sa aure kan kai shekara 45 ko yaji mace batai ba.

2* AZAMANIN DA MAFIYA YAWAN MATASA ANAYI MUSU AURE KO SUNAYI BADAN SHA'AWABA.
dayawa ma wasu yimusu akeyi zakaga su sunyadda aure ibadane ,wasu sundauka alamace ta yaro yagirma hakan tasa da yaro yabalaga za ayimasa aure badan sha'awaba DOMIN SAURAYIN MA BAI IYA SAKEWA YAYI SHIRA DA BUDURWA HAKA ITAMA SUNA JINKUNYAR JUNANSU KO SHIRA SUKE SAI KAGA TSAKANIN SAURAYI DA BUDURWA SAI MOTA BABBA TAZO TAWUCE TASTAKIYARSU. WASUMA TA TSAKANIN DANGA AKEYIN SHIRAR TARE DA CEWA SUNASON JUNANSU ,DAN ZAKAJI BUDURWA A DANDALI GUN WASA TANA WAQE SAURAYINTA. hakama in anyi auren wani saurayin sai yai wata guda bai shiga dakin amaryarba ballantana ma ya kwanta da ita waishi kunya yakeji hakan ,daman badan sha'awa akai auren ba. AMMA ABUN HAUSHI A YAU MAFIYA YAWAN MATASA SUNAYIN AURENE DAN SHA'AWA BAWAI DAN IBADANE BA, inkadubi yadda ake shira tsakanin saurayi da budurwa a yau zakasan shirace ta motsa sha'awa da son kusantar juna ,dazarar anyi aure ANGO HAR KORAR ABOKAI YAKEYi YAN RAKIYA ZUCIYAR SA CIKE DA SON WANI ABU HAKA ITAMA AMARYAR ,saikaga wata 6 dayin aure bayan matashi yagama kashe sha'awarsa da amarya ga dawainiyar aure kuma sai yafara batamata rai ko itatabata masa rai daganan sai fada da yaji ,
TO DAMA WAHALA DA MASIFUN BIDIO IN AURE SUNSA BAI YI AURE DA WURIBA YA ZAMA QATON BALIGI YATARA SHA'AWA IDONSA YARUFE KOWACCE MARAR TARBIYYAR DAYAGA JIKI SAI YAGA TAYI MASA DOMIN SU MATASA MAFIYA YAWANSU SHA'AWACE MA AUNIN SU NASO ,WATO DAYAGA BUDURWA YAJI TAYI ARANSA SHIKENAN.

yana da kyau anayin aure dan Allah dan kuma shi'ibadane da kariya gareka da ita matar bawai dan sha'awaba. Dakuma rage buri da munanan al'adun aure na bidio'i da rashin tunani .

*3 AUREN DA NAGARTA AKEBI:
SAMARIN DANA NAJIN MAGANAR IYAYENSU danhaka sukuma iyaye nagarta suke bi ,sune suke zabawa SAURAYI BUDURWA KO BUDURWA SU ZABAMATA SAURAYI DAGA BAYA ACE SAURAYI YAJE YAGANTA SUYI SHIRA ,kuma ayimusu aure su zauna lafiya ,wani ma baya garin za ayimasa amma dayazo in yai biyayya sai Allah yasa son juna da tausayi saikaga sunzauna shekara sama da 56 ko yaji bata tabayi ba AMMA A YAU SAURAYINE ZAI ZABO DAKAN SA KODA NAGARTA KO BABU SHIDAI INDAI AKWAI JIKI KO TA IYA MAGANA ,KO KWALLIYA DA DAI SHAURAN SU DAYAWA MATASA BASUFIYA DAMUWA DA HALAYEBN BUDURWABA saikaga saurayi yazabo budurwa da kansa amma anyi aure shekara 1,-o 3 an rabu,

*4 ADA ANAYIMA MATASA AURE DA WURI KAFIN BALAGA TA TSANANTA AGARESU ,amma yanzu matashi ba afiya yimasa aureba sai dai yayiwa kansa, HAKAN TASA MATASA MAZA DA MATA SUN GAMA BALAGA SUNA CIKIN MAWUYACIN HALI NA SHA'AWA amma wasu buri yahanasu .wasu kuma ba yadda zasuyi saboda tsadar rayuwa.da halin yau.

Allah yasa mugyara halayen mu YA ALLAH KABAWA MATASAN MU ARZIKI ME ALBARKA KABASU ABOKAN ZAMA NAGARI.

No comments:

Post a Comment

https://shaykhulislaam.files.wordpress.com/2010/12/criterion.pdf

https://shaykhulislaam.files.wordpress.com/2010/12/criterion.pdf