jerin bayanai

Friday, 6 October 2017

QALUBALEN KU IYAYE: 0907371728

QALUBALEN KU IYAYE:


yana daga haqqin YARKA A KANKA kazaba mata miji nagari,
AMMA ABUN MAMAKI A YAU ZAKAGA IYAYE SUN ZUBAWA YAYAN SU MATA IDO ,SU NE KE ZABAWA KANSU MIJI .sukuma iyayen batare da wani binciken kirkiba sun dau budurwa kawai sun bawa SAURAYI BATARE DA TANTANCE.
**MEYE AQIDAR SA BA,YA HALATTA ABASHI BAI HALATTABA OHO
**YANA DA MUGUN HALI KO BABU?
**MUTUMIN KIRKINE KO BANA KIRKINE BA.?
a a su iyaye kawai da zarar sunga me kudine shikenan sai kaga daga yarinyar har iyayenta SUN RIKICE IDON SU YARUFE ,HAKA ZASU DAU YARINYA SUBASHI.SAI DAGA BAYA ANSAMI MATSALA KAGA BUDURWA TA ZAMA ABAR TAUSAYI.
***ILLAR AURAR DA MACE BATARE DA ANYI BINCIKEN WAN DA ZAI AURETABA**
1* MATSALA A IMANINTA:
an samu dadama mace an aurar da ita ga wanda bai da aqida me kyau .ANSAMU ANAN KANO INDA NAKE wani saurayi yazo ya auri wata budurwa IYAYENTA basu yi kwakkwaran bincike ba suka bashi ita wlh kafin haihuwar fari ya maida ita Yar shi ah.
*2*ansami wadda ya aurI wata budurwa itama ba ai bincike sosai ba anan kano ASHE DAN SHI AH NE. yaboye aqidarsa sukuma iyayen ta basu yi binciken kirkiba a qarshe ZAI YI TAFIYA KAWAI YAKAWO MATA ABOKIN SA DAN SHI AH,DAN YA KWANA DA ITA (aron farji ) .ALLAH YASA ME TARBIYYA CE TAQI YADDA DASHI TAFADAWA IYAYENTA AKA RABA AUREN ,HAR KOTI ANA SHARI AH
*3*AN SAMU DAYAWA MUTUM AN AURA MASA MACE DAGA TA HAIHU ,YAGUDU YABARTA BA ASAN HAQIQANIN GIDANSU BA.
*AKWAI WATA BAIWAR ALLAH,a kano a wata unguwa yakasai tana karatu tagama n.c.e 1 miji yafito mata wani soja ne AMMA ABUN HAUSHI AURI SHIKA YAKEYI,wlh shekara 1 ya sauta DA CIKI kuma awulaqance ,bai barta tayi karatuntaba ba bai kuma riqeta amana ba..
* YAN UWA AKWAI MUSALAI DAYAWA NA IRIN WADANNAN MATSALOLIN*
SHAWARATA GAREKU IYAYE
*kudena gaggawar daukar budurwa ku bada ita ga wanda bakusan aqidarsa ba,halayen sa.UMAR NINE NA ANNABIN RAHAMA S.A.W
cewa idan wanda kuka yadda da addininisa(aqidarsa halayyasa a addini) yazo neman auren yarku to kubashi .inkuma kuka hanashi to zaku haifarda fasadi abayan qasa.
KUNGA KENAN MUTUM NAGARI AKEBAWA AURE.
*KADA KAQOSA DAN KAGA YAR KA BATA SAMI MIJI DA WURIBA .YIMATA ADDU AH ALLAH YABATA NAGARI,dan kome da lokacinsa ,kakwantar dahankalinka kacigaba da bata kulawa ,tarbiyya har asami nagari.
*DOLE iyaye kurage kwadayi kuna aurar da yayan ku ga mutanen kirki KODA TALAKAWA NE MATUQAR YANA DA HALAYE NAGARI, DA ZUCIYAR NEMAN HALAL DINSA
*SA IDO AKAN YADDA YARKA TAKE GUDANAR DA SOYAYYARTA DA SAURAYI DA ZARAR YAFARA ZUWA , KA BINCIKI YADDA DA AQIDARSA TAKE NAKIRKINE KO BANA KIRKINE BA SHIKENAN INKUWA BAI DA AQIDA ME KYAU SAI KA HANASHI TUNKAFIN YA SACE ZUCIYAR YARINYAR KA ,TAIMA TAWAYE.
kana iyayin bincike tahanyar dabara bata yadda zai tsarguba koda tabayan fage ne YIN BUNCIKE A AURE UMARNINE NA ANNABIN RAHAMA S.A.W
*YAWAITA ADDU AH ,DA BINTSARIN MANZON RAHAMA S.A.W
***YAR UWA KI RABU DA RUDIN DUNIYA KITSAYA KINUTSU KIZABI MIJI NAGARI WANDA ZAI ZAMEMIKI DIREBA A RAYUWARKI ,WANDA ZA KI BAWA ZUCIYARKI KYAUTA DOLE YAZAMA ME AQIDA TAGARI BAWAI KAWAI DA KINGA MOTA,KO KUDI BA.,KIRIKICE SAI KIGA KIN AURI WANDA ZAI TA GASAKI HAR KI MUTU AHAKA.
Sannan kituna saikinzama tagari Allah zaibaki miji nagari kema
ALLAH YAIMANA AFUWA.

No comments:

Post a Comment

https://shaykhulislaam.files.wordpress.com/2010/12/criterion.pdf

https://shaykhulislaam.files.wordpress.com/2010/12/criterion.pdf