jerin bayanai

Sunday, 8 October 2017

YADDA YAKAMATA YAR UWA KIYI CHATTING IN BAZAKI IYA HAQURABA. 09073717289

YADDA YAKAMATA YAR UWA KIYI CHATTING IN BAZAKI IYA HAQURABA.

YAZAM Dole ki tsare mutuncin kanki da na maigidanki da kuma na iyayenki a yayin da kike amfani da wadannan kafofi kamar yadda za ki tsare a fili, don haka duk wata hira, ko wani sakin fuska, ko shige-shige da wani kawance da kika san aikata hakan a fili zai zubar da mutunci mijinki ko na iyayenki, GA YADDA YADACE KIYI
*1* Tantance Abokan Hulda: Dole sai kin yi matukar taka tsan-tsan da lura sosai ga mutanen da za ki yi hulda da su a wannan kafa: Mata kadai ya halatta ki rika amsa ko aika ma sakon amintaka WATO QAWANCE, kuma su ma matan wadanda kika sani kadai, domin akwai da yawa mazan da ke amfani da sunan mata kawai don yaudara SUNEMA MAFIYA YAWAN MATA A SOCIAL NETWORK
*2* Duk namijin da za ki yi hulda da shi, to ki tabbata dan uwanki ne ko kuma wani da kika sani da dadewa, sannan za ki yi hulda da shi ne ta hanyar kara wa juna sani a kan al’amuran addini da wayar da kai kadai. Ba ruwan ki da yawan gaisawa da su ko yin hirar yaushe rabo ko yawan tambaye-tambaye. Idan suka dame ki da yawan tambaya da son hira, sai ki yi shiri ki kyale su, domin ba su da damar da lallai sai kin amsa musu.
*3*IN KE BUDURWACE KYA IYA QAWANCE DA NAMIJIN DAKIKA JARRABASHI KIKAGA NA KIRKINE ,amma kuskurene kodake budurwace ki tara samari wai da sunan friend IN WANNAN BAYANAN KIYI DAWANNAN INA WANCAN BAYANAN KIYI DA WANCAN KUMA,BA WATA SHIRAR KIRKIBA ,BAKUMA SAURAYINKI NAGASKIYABA AKWAI SHIRME DA BATA LOKACI,DA YAUDARA
*4* Duk wani dandali ko shafin da za ki shiga, to ki tabbata wanda zai zama mai alfanu ne a gare ki, wanda zai kara miki ilmi da wayar miki da kai ta fannin addini da zamantakewa ne; duk wani dandalin bayan kin shiga, kika lura ana abubuwan da ba su dace da addini ba, ko ana sharholiya da sabon Allah, to ki yi maza ki fita daga cikinsa.
*5* Duk namijin da ya aiko miki da wani sakon wasika, to kada ki amsa masa ko da kuwa da amsa sallama ne, domin duk namiji mai mutunci ba zai je yana yin magana da matan da ba muharramansa ba a wadannan MATUQAR YASAN KE MATAR AURECE. Don haka sai ki yi hanzarin kange duk wani namijin da ya aiko miki sakon wasika ko ya dame ki da yawan gaisuwa; wannan ba alheri yake nufin ki da shi ba, masinjan shaidan ne da ya aiko don ya ja ki ga sabon Allah.
*6*Haramun ne sanya hotunanki ko da kin sa hijabi da nikabi kin rufe fuskarki, domin na farko wannan ba wani alfanun da zai kawo miki ke da kika sanya hotunan ko wadanda suka kalli hotunan naki. Hasali ma yana iya zama sanadiyyar jefa ki cikin wata matsala.
*7*Ki yi taka tsan tsan wajen sanya hoton yara kanana, naki ko na kawaye ko na ’yan uwa, duk da cewa hakan ba haramun ba ne, amma ya kamata a kiyaye, doMIN HOTAN NA IYA FADAWA HANUN WANI SHASHASHAN YAI TA YADASHI,KOWANI MA YAIMASA BAKI
*7*Ki yi matukar taka tsan-tsan, kada ki rika tallata ni’imomin da Allah Ya yi miki a wadannan kafofi: kamar ki rika labarin zaman jin dadin da kuke yi da maigidanki; ko ki rika bagu da wata baiwa ko wani arziki da Allah Ya yi miki; ko ki rika bayyana abubuwan burgewar da ’ya’yanki suka yi. Za ki yi hakan ne don guje wa sharrin zuciya da tunanin wasu mutane, domin idan kika rubuta kika watsa ba ki san iyakar inda wannan rubutu zai je ba, kuma ba kowane mutum ne yake da tsarkakkiyar zuciya marar hassada ba. Hassadar wasu mutanen ga abubuwan alherin da kika tallata na iya janyo miki hasarar wadannan abubuwa ba tare da kin sani ba.
*8*Tsare Mutunci Maigida: Yana da matukar muhimmanci ki tsare mutuncin maigidanki a wadannan kafafe, duk wani namijin da ba muharraminki ba, to babu ruwanki da shi, kada ki yarda wani namiji ya rubuta wani abu ki nuna wannan abun ya burge ki (wato ki yi liking) ko da kuwa ya burge ki din; domin wannan zai bude hanyar da shi wannan namijin da ba muharraminki ba zai miki magana; wani ma sai ya ga don ya kula ki shi ya sa kika aikata hakan.
*9*TUN FARKOMA DAMAN BAZAKIYA CHATIN BA HAR SAI DA YARDAR MEGIDANKI IN YAHANAKI DOLE KI HAQURA IN YA AMUNCE TO ina ba ki shawarar ki sanar da SHI WATO maigidanki makullinki na shiga wadannan SOCIAL NETWOK DIN WATO PASSWOR DA USERNAME,HAKAN ZAI SA YANA DUBAWA MEKIKE AMFANUWA DASHI,SUWAYE ABOKAN HULDARKI KUMA BA ZAI ZARGEKIBA, kuma ki karfafa masa gwiwar ya rika budewa a-kai-a-kai yana ganin irin yadda kike amfani da su, inda ya ga kin yi kuskure, ko ya ga wani abu da bai dace ba, sai ya tunatar da ke. Wannan zai zama wani samfurin tsaro ne gare ki na ba za ki rika wuce iyaka ba, komin yadda dadin amfani da wadannan kafafe ya debe ki, domin kin san akwai yiwuwar wata rana maigidanki zai bude ya gani. Hakan kuma zai tabbatar wa maigidanki zama tsayayye gare ki ta kowace fuska da kowane bangare na rayuwarki.
*10*KIZAMA ME KAWO ABUBUWAN AMFANI GA YAN UWANKI MATA MUSALI ,NASIHA,KOYA GIRKI,ZAMANTAKEWA DA SHAURAN ABUBUWA.
***SHAWARA GAREKI YAR UWA KI HAQURA DAYIN AMFANI DA KOWACCE SOCIAL NETWORK SHI YAFI KUSA DA TSORAN ALLAH DA ZAMA MUMINA ,IN BAZA KI HAQURABA KO MIJINKI YA BARKI TO GA HANYOYIN DAYAKAMAT KIBI,
MUJI TSORAN ALLAH IYA IYAWARMU***

No comments:

Post a Comment

https://shaykhulislaam.files.wordpress.com/2010/12/criterion.pdf

https://shaykhulislaam.files.wordpress.com/2010/12/criterion.pdf