jerin bayanai

Thursday, 12 October 2017

a yayin da so kekoqarin shiga zuciya 09073717289

Ayayin da so ke kokarin shiga zuciyar wadda yaga yakan fara ne da satar kallon wannan abun tare da qare masa kallo adai dai wannan lokacin zuciyar wanda keyin kallon cike take da farggaba dan kar wanda yake kallo ya waiwayo, dazarar ya waiwayo zaiyi sauri ya kau da kai kodai yai fuska ko yayi murmushi dazarar an yi ido hudu da juna sai zuciya taji an kwaramata wani sanadari me kwaranyowa daga saman qirjinta zuwa qasa tamkar an zare mata laka ,daganan zuciya zatafara dan karan tunani akan sa me zafi da sanyi.
Kamar Gaskiya yana da kyau , ko yafiye baqi ,kawai abu dayane yai masa cikas ,in naso shi mundace ,gaskiya ni ba sa arsabace haka dai zuciya zatai ta tunanai.
Hankali da hangen nesa shine malamin dake tabbatarwa da zuciya soyayya da tahanyar tantance ingancin abin so bisa la akari da me zuciya take so.

Dazarar zuciya takamu so yayi loggin in sai kome nata yacanza.

Saimucewa wannan zuciyar barka da zuwa duniyar masoya, me cike da mayen soyayya wadda mayenta yafi na zuma bare sukari wane madara ,duniyar tunani da damuwa in ansami matsalat ,

amma in komai yatafi daidai baka iya kwatanta dadi da farincikin da masoya keji a zukataan su ba.

A lokacin da masoyan juna biyu suka hadu tare da misayar kallo nantake wata jazabar so ke lullube su tare da cillasu cikin kogin shauki cikin sai sujisu tamkar ba wasu masoya sai su, sukan manta da wanda ke kusa dasu.
Dazaka sa na urar leqa zuciya dakaga kifiyoyin sanadaran haske na fita daga wannan zuciya zuwa wannan zuciya.

Aduk lokacin da hasken kifiya ya soki zuciyar abin sonsa nantake farinciki da annashuwa ke sauka tare da mamaye dukkan sassan jiki masoya

nandanan karshashi ke sake haifar da wani kallo na daban wanda ba wanda akewa irin wannan kallon sai masoyin na hakika,kallone da baifi second biyu ba batare da qifta ido ba nantake dukkan wata damuwa ke gushewa daga zuciyar nantake fuskar masoya ke canjawa tana wana sheki da walwali tamkar tacaccen zinare dake haskakawa a tsakiyar rana.
Batare da bata lokaciba masoya zakaga sun sake kallon juna tare da sakar wani tautausan mursmushi me sa zuciya wata irin nutsuwa ta musamman ,

tabbas masoya kadaine ke iya musalta dadi da shauqi da jazabar da sukeciki a irin wannan yanayi.

A irin wannan yanayin komai masoyi yayi daidaine agun abun qaunarsa.
Dazarar masoyi ya buda tausasan lebbansa ya furta kalmar so wayyo ba abunda yafi jin wannan kalmar dadi musamman ma irin yanayin da aka furtata cikin nutsuwa ,murmushi kallon kayimin kuma dan shine kadai aka furtata nantake masoyi zaiji yafi kowa dace da abun qauna.

Musali Aishat hade da murmushi da kallon idanun masoyiya.

Ko zainab kinsan me humm wlh ina matuqar sonki

ko hafsat ina sonki

wadannan kalamaine me matuqar ratsazuciyar wadda akafurtawa da wanda yafurta.

IDAN AKA SAMI AKASI A DUN
IYAR SOYAYYA TO BA DUNIYAR DATAFITA ZAFI ,DIMUWA,AZABA DA ZAMAN KASO.


Gane haqiqanin so da soyayya sai dai Allah domin al'amuran soyayya tamkar kojine kowa shiga yake yayi iya iyawarsa yafito.

Samun soyayyar abu abune me wahala a mafiya lokaci domin yakan dau lokaci kafin aji anasonka musammanma ba asankaba.

Al amarin mace a soyayya kawai kaifi dayane intana sonka to tana sonka inbata sonka kawai bata sonka oda kun kai ku goma samarinta TO DAYA TAKE KALLO A MATSAYIN TAURARO shauran kawai tamkar shauran mutanen gari take ganinku koda kana shan kalaman soyayya daga gunta iya baka ne kawai kodan kwadayin abun hanunka.

Ba abun mamaki bane mace dan tafi son soyayya da shira da saurayi me iya kalamai DOMIN ANNABIN RAHAMA S.A.W YACE ACIIN ZANCE AKWAI SIHIRI.

mata sunfi maza shiga takura da qunci in soyayya tai gardama ,mazakuma sunfi yanke mummunan hukunci idan soyayya tai gardama.

Sautari namiji meyawan yan mata baifiya auren zabin ransaba wato sai qasa da ajinsa.

Budurwa e ruwan ido qarshenta tarihin soyayyarta nadama

damutane sun san sirrin dake tattare da matan kauye da na burni sunyi kwantai.

Me haquri shiyafi kowa cin ribar soyayya.hakanan wanda yafika iya soyayya tabbas zai iya rabaa da masoyiyarka.

Mata basufiye hangen yadda soyayyar su zata kasance a nangaba ba SUNFI DUBAN MATSAYIN TA A YANZU
09073717289

No comments:

Post a Comment

https://shaykhulislaam.files.wordpress.com/2010/12/criterion.pdf

https://shaykhulislaam.files.wordpress.com/2010/12/criterion.pdf