jerin bayanai

Thursday, 12 October 2017

so tsuntsune 09073717289

SO TSUNTSUNE:

wannan azancin maganane tun iyaye da kakani kuma sanannan abune shi so tsuntsune ABUNE ME METUQAR MUHIMMANCI MUYI NAZARI AKAI KODA KADANNE MEYASA AKA DANGANTA SO DA TSUNSTSU?

tabbas dukkan wanda yasan dabi'ar tsuntsu to yasanshi da alqawari akan bishiya wato in tsuntsu tazo yai gida akan bishiya zaiwuya atashe shi daga wannan bishiyar ko ruwa ko rana saidai yaita gyara wannan gidan nasa KODA RUSAMASA SHI AKAYI , AMMA RANA A TSAKA KAWAI GANIN DAMAR SA SAI KAGA YATASHI DAGA WANNAN BISHIYAR WACCE GIDANSA YAKE KAI YAKOMA WATA YANA KUMA QOQARIN NEMAN GURBIN DA ZAI GINA WANI GIDAN KOMAI RASHIN KYAN WANNAN BISHIYAR KO HATSARINTA SHI SAM BAIDAMU BA haka zai koma kanta.

Meyakesa tsuntsu yin hakan ?
* buqatar son ransa
amma bawai dan ba abunci ba kodan abunci yayi yawaba domin tsuntsu yakan iya yima tafiya kusan kano to kaduna yaciko qundunsa yakuma dawo bishiyarsa ta ainashi baidamu ba.

Tabbas kalmar so itama tana da wadannan halaye MACE KAN IYA SON SAURAYI TSAHON LOKACI SAIKAGA KUMA RANA A TSAKA SO ANNE MESHI AN RASAHI sai kaga kuma yakoma kan wani watakilama ba azataba saikaga shi ake so koda bai kai wancan dinba inganci.

MEYASA HAKAN TAKE FARUWA?

* buqatar zuciya.
Wataqila dama can maleji takeyi dakai dan baka cika sharudan da take so saurayinta yazama yana dasu ba amma kana da kaso 50 cikin dari wataqila me ilmi take so ko me kudi ko danboko ko me haquri ko gaye ko ustaz Amma kuma kai duk rabinsu ne. Tofa dazarar taga wanda yake da wadannan sharudan nata saitaji ya kwantama a rai zucciyarta ta amunta dashi daganan zatafara sonsa ko a boye ko afili koda baida ingancin wancan.

* canjawar hali daga abunda akeso .IDAN YAZAMANA WANI DALILINE YASA AKE SONKA KAMAR ADDININKA ,KUDINKA HAQURINKA sai kuma ka canja kazama marar su tofa ananma so zai iyayin qaura daga kankan zuwa wanninka.

2 TSUN TSU YAKAN IYA TASHI DAGA KAN KOWACCE BISHIYA ZUWA WATA BISHIYAR KOWACCE YACIGABA DA SHA ANINSA.

hakama so idan wadancan dalilan suka faru yakan iya tashi daga kan qani yakoma kan yaya koda yaya yakoma kan qani ,daga da yakoma kan uba ,daga saurayi ya koma kan abokin saurayi ya,koma kan qawar budurwa.daga qanwa zuwa yaya
Batare da duba alaqar ko dangantaka dake tsakani ba.

MUSALI DAGA LABARI NAGASKIYA

akwai wata budurwa sunannata khadija da tana da saurayi suna soyayya yama turo iyayensa angama komai yakaimata akwati 2 dakudin aure AMMA RANA A TSAKA WANI MALAMI DAGA CIKIN MALAMAN MAKARANTAR ISLAMIYYAR SU yace yana sonta ,shikenan ta amunce masa soyayya wallahi kamar sunyi shekara.
Iyayenta sunyi sunyi taqi haqura takawo musu hujjojinta kuma sungamsu da ita
na 1 tace shi nafarko bashi da ilmin addini ITAKUMA KOWA YASAN YARINYAR DA SONKARATUN ADDINI tace ko sunyi aure yadinga biyamata karatu.

2 wannan yayi karatun boko har n c e amma shi nafarko iya sakandire yayi.

Tare dacewa shi wannan malamin da takeso bashi da sa na'a ta kirki.
Amma dukdahaka ita bata gahakaba tunda yana da ilmi kawai yacika sharudanta.

2* labarin haris da abokinsa bashir

bashir yanada buduwar amina suna soyayya rimi rimi watarana yakai abokinsa haris ,shikuma haris mutumne me surutu da tsokana da wasa da bandari.
Ranar farko da yaraka bashari gun amina SAI DA YASATA DARI DA NISHADI ,tundaga ranar baiqara raka bashirba domin yana zuwa zage kasuwa. Amma kullun bashir yaje shira SAI AMINA TACE MASA INA BASHIR KAQI ZUWA DASHI

har bayan sati tazago bashir yasake tawowa da haris gun amina sukayi shira sosai KAI NA TAQAICEMUKU HAKA AKAI TAYI HAR BASHIR YAFARA TSARGUWA har aqarshe amina tafarayiwa bashir kora da hali take kuma nunawa haris soyayya ita wallahi dashi sukafi dacewa kaima haris kasani
ALLAH YASA HARIS DIN ME HANKALINE YADENA ZUWA GUNTA MA DUKKA.

tabbas mace tana da wata illa takan iyayin soyayya da kai ta maleji koda bata sonka kafin tasami wani zabin ranta IDAN KAYI RASHIN SA'A KA AURIMACE A SOYAYYAR MALEJI TOFA KASHIGA UKU tun awatannin farko zakufara samun matsala aita mamaki meyakawo haka bayan auren soyayya akayi AMMA SU QAWAYENTA AMINANTA SU SUNSAN DAMA KAWAI TANA SOYAYYA DASHINE DAN BATA DA WANI SAI SHI.
amma wayayyiyar budurwa kuwa kaifi dayace in tana sonka kawai to tana sonka inbata sonka to bata sonka kawai saidai ko dan abun hanunka.
LALLAI SO TSUNTSUNE

No comments:

Post a Comment

https://shaykhulislaam.files.wordpress.com/2010/12/criterion.pdf

https://shaykhulislaam.files.wordpress.com/2010/12/criterion.pdf